Labaran Kano – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com ...Muryar Jama'a Sun, 07 Jun 2026 17:51:52 +0000 en-GB hourly 1 https://i0.wp.com/freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Freedom-Kano-e1568718728160.png?fit=32%2C32&ssl=1 Labaran Kano – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com 32 32 166714237 Gwamnatin Kano ta dakatar da sare bishiyoyi a harabar gidan talabijin na jihar ARTV https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ba-da-umarnin-dakatar-da-sare-bishiyoyi-a-harabar-gidan-talabijin-na-jihar-artv/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ba-da-umarnin-dakatar-da-sare-bishiyoyi-a-harabar-gidan-talabijin-na-jihar-artv/#respond Sun, 07 Jun 2026 19:46:42 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59377 Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da sare bishiyoyi ba tare da ka’ida ba a harabar gidan talabijin na jihar, Abubakar Rimi Television (ARTV), bayan wani bidiyo da ya karade  kafafen sada zumunta yana nuna yadda ake sare bishiyoyin.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayar da umarnin yayin wata ziyara ta bazata da ya kai tashar a ranar Asabar.

Ya ce sare bishiyoyin ya saɓa wa manufofin gwamnatin jihar na kare muhalli da yaƙi da sauyin yanayi, tare da gargadin cewa daga yanzu ba za a sare kowace bishiya a tashar ba sai an samu amincewar hukumomin da abin ya shafa.

Waiya ya kuma nuna damuwa kan yadda tashar ke gudanar da ayyukanta, yana mai cewa shirye-shiryenta da labaranta ba sa gamsar da masu kallo saboda rashin sabunta abubuwa da kuma ƙarancin ingancin labarai.

Ya bayyana cewa zai miƙa rahoto na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin neman tallafi na musamman don inganta tashar da kuma mayar da ita ta zamani.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ba-da-umarnin-dakatar-da-sare-bishiyoyi-a-harabar-gidan-talabijin-na-jihar-artv/feed/ 0 59377
Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin yashe magudanan ruwa domin kaucewa ambaliya https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-shirin-yashe-magudanan-ruwa-domin-kaucewa-ambaliya/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-shirin-yashe-magudanan-ruwa-domin-kaucewa-ambaliya/#respond Thu, 04 Jun 2026 15:08:54 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59309 Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin yashe magudanan ruwa a fadin jihar gabanin saukar daminar bana ta 2026.

 

Kwamishinan ma’aikatar Muhalli, Al’barkatun Ruwa da Sauyin Yanayi na jihar Kano Dr. Dahiru Muhammad Hashim ne ya jagoranci kaddamar da shirin a yankin Jakara da ke Karamar Hukumar birni a jihar Kano a ranar Al’hamis 04-6-2026.

Kwamishinan ya ce an bijiro da shirin yashe magudanan ruwan ne domin kaucewa ambaliyar ruwa a cikin unguwannin da ke kewaye da manyan kwatoci.

Haka zalika ya kara da cewa, gwamnati zata cigaba da gudanar da wannan aiki a fadin jihar Kano baki yada.

 

A karshen ya nemi hadin kan al’umma domin bayar da cikakken hadin kai a yayin gudanar da aikin.

 

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-shirin-yashe-magudanan-ruwa-domin-kaucewa-ambaliya/feed/ 0 59309
NSCDC ta kori jami’an sa-kai biyar a Kano saboda rashin ɗa’a https://freedomradionig.com/nscdc-ta-kori-jamian-sa-kai-biyar-a-kano-saboda-rashin-%c9%97aa/ https://freedomradionig.com/nscdc-ta-kori-jamian-sa-kai-biyar-a-kano-saboda-rashin-%c9%97aa/#respond Tue, 02 Jun 2026 14:37:15 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59252 Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta kori wasu jami’an sa-kai biyar daga aiki bisa zargin rashin ɗa’a, rashin ƙwarewar aiki da kuma aikata abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idojin hukumar.

 

Mai magana da yawun hukumar a Kano, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. Ya ce kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya amince da korar jami’an ne bayan an binciki laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

 

Jami’an da aka kora sun haɗa da Yakubu Mubarak Yusuf, Isma’il Muhd, Adamu Auwalu, Abdulrazaq Suleiman da Ahmad Sarki. Hukumar ta ce ta kwace dukkan kayan aiki, kayan sawa da katunan shaidar aiki da suke amfani da su.

 

Kwamandan ya kuma umarci dukkan shugabannin yankuna da na ofisoshin hukumar a faɗin jihar da su tabbatar da cewa ba a sake bai wa waɗanda aka kora wata dama ta wakiltar NSCDC ba. Ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani hali da zai zubar mata da mutunci ba, yana mai cewa duk wanda aka samu da irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukuncin da ya dace.

]]>
https://freedomradionig.com/nscdc-ta-kori-jamian-sa-kai-biyar-a-kano-saboda-rashin-%c9%97aa/feed/ 0 59252
Gwamnatin Kano ta haɗe Ma’aikatar Ruwa Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata guda https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ha%c9%97e-maaikatar-ruwa-muhalli-da-sauyin-yanayi-zuwa-maaikata-guda/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ha%c9%97e-maaikatar-ruwa-muhalli-da-sauyin-yanayi-zuwa-maaikata-guda/#respond Tue, 02 Jun 2026 07:57:09 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59239 Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haɗe Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata guda ɗaya mai suna Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi. 

Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na inganta gudanar da ayyuka da kuma haɗa ƙarfi wajen magance batutuwan da suka shafi ruwa, muhalli da sauyin yanayi a jihar.

A wata sanarwa da Kwamishinan sabuwar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim ya fitar, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da haɗe ma’aikatun biyu tare da naɗa shi a matsayin wanda zai jagoranci sabuwar ma’aikatar.

Dakta Dahir Hashim ya bayyana cewa shi da tawagarsa sun shirya tsaf domin tabbatar da sauyin ya gudana cikin nasara, tare da ƙarfafa ayyukan da suka shafi kula da muhalli, yaƙi da illolin sauyin yanayi da kuma inganta sarrafa albarkatun ruwa domin amfanin al’ummar Jihar Kano.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ha%c9%97e-maaikatar-ruwa-muhalli-da-sauyin-yanayi-zuwa-maaikata-guda/feed/ 0 59239
Gwamnatin Kano za ta kawo karshen matsalar ruwan sha kafin karshen shekarar 2026 https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-za-ta-kawo-karshen-matsalar-ruwan-sha-kafin-karshen-shekarar-2026/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-za-ta-kawo-karshen-matsalar-ruwan-sha-kafin-karshen-shekarar-2026/#respond Mon, 01 Jun 2026 13:42:04 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59232 Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da kudurinta na kawo karshen matsalar rashin ruwan sha da al’ummar jihar ke fuskanta, ta hanyar kammala manyan ayyukan gyaran hanyoyin samar da ruwa da kuma inganta rumbunan adana ruwa a sassan jihar kafin karshen shekarar 2026.

Mukaddashin Kwamishinan Ruwansha na jihar Kano, kana Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin rangadin duba aikin gyaran rumbun ajiyar ruwa na Gwauran Dutse da ke cikin birnin Kano.

A cewarsa, jihar Kano na da isasshen ruwa da zai wadatar da al’umma baki daya, amma matsalolin lalacewar kayan aikin samar da ruwa da kuma sace-sacen na’urorin rarraba ruwa ne suka haddasa karancin ruwan sha a wasu yankunan jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na gyara manyan rijiyoyi, rumbunan adana ruwa da kuma hanyoyin rarraba ruwa domin tabbatar da cewa al’ummar Kano sun samu wadataccen ruwan sha.

Ya kara da cewa ana ci gaba da aikin gyaran rumbunan adana ruwa masu daukar miliyoyin lita na ruwa, kuma gwamnati na sa ran kammala ayyukan cikin wa’adin da aka tsara, lamarin da zai taimaka wajen magance matsalar karancin ruwa musamman a cikin birnin Kano da kewaye.

Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kare kayayyakin gwamnati da ake amfani da su wajen samar da ruwa, tare da kai rahoton duk wani yunkurin lalata ko sace kayan aikin domin tabbatar da dorewar ayyukan samar da ruwan sha.

Ya jaddada cewa da zarar an kammala wadannan ayyuka kafin karshen shekarar 2026, matsalar rashin ruwan sha a mafi yawan sassan jihar Kano za ta zama tarihi.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-za-ta-kawo-karshen-matsalar-ruwan-sha-kafin-karshen-shekarar-2026/feed/ 0 59232
Rundunar Anti Phone Snatching ta sanar da dakatar da ayyukanta a Kano https://freedomradionig.com/rundunar-anti-phone-snatching-ta-sanar-da-dakatar-da-ayyukanta-kano/ https://freedomradionig.com/rundunar-anti-phone-snatching-ta-sanar-da-dakatar-da-ayyukanta-kano/#respond Sat, 09 May 2026 08:56:44 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58983 Hukumar da ke yaƙi da kwacen waya ta Anti Phone Snatching ta sanar da dakatar da ayyukanta baki ɗaya a faɗin jihar Kano, sakamakon abin da ta bayyana da rashin biyansu haƙƙoƙinsu na tsawon shekaru.

‎Mambobin ƙungiyar sun bayyana hakan ne a zantawarsa su da manema labarai, inda suka nuna damuwarsu kan halin da suke ciki duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da masu kwacen waya da sauran masu aikata laifuka.

Hukumar ta ce matakin dakatar da aikin da ta ɗauka zai ci gaba har sai gwamnatin ko hukumomin da abin ya shafa sun biya su haƙƙoƙinsu tare da duba koken da suke yi.

]]>
https://freedomradionig.com/rundunar-anti-phone-snatching-ta-sanar-da-dakatar-da-ayyukanta-kano/feed/ 0 58983
Gwamnan Kano ya zabi Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin sa https://freedomradionig.com/gwamnan-kano-ya-zabi-murtala-sule-garo-a-matsayin-mataimakin-sa/ https://freedomradionig.com/gwamnan-kano-ya-zabi-murtala-sule-garo-a-matsayin-mataimakin-sa/#respond Wed, 22 Apr 2026 04:04:30 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58746 Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Alhaji Murtala Sule Garo zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Hakan na cikin wata sanarwar da Sakataren Yada Labaran gwamnan, Malam Mustapha Muhammad ya fitar a tsakar daren yau Laraba 22 ga watan Afrilu 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa zabar matakin ya yi daidai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya ba gwamna damar nada mataimaki idan an samu gurbi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa kujerar ta zama babu kowa ne bayan murabus din da tsohon mataimakin gwamna, Comrade Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris 2026.

Murtala Sule Garo mai shekaru 48 ya taba rike mukamai daban-daban a gwamnati da siyasa, ciki har da kwamishina baya ga shugaban karamar hukuma.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnan-kano-ya-zabi-murtala-sule-garo-a-matsayin-mataimakin-sa/feed/ 0 58746
Gwamnatin Kano ta bukaci Sarakunan jihar su shirya addu’o’in zaman lafiya https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bukaci-sarakunan-jihar-domin-yin-adduoin-zaman-lafiya/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bukaci-sarakunan-jihar-domin-yin-adduoin-zaman-lafiya/#respond Sat, 11 Apr 2026 08:33:56 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58592 Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci dukkanin sarakuna, dagatai da masu unguwanni da su mayar da hankali wajen gudanar da addu’oin domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamnan ‎ya bayyana hakan ne da yammacin jiya juma’a yayin wata ziyarar ta’aziyyar mahaifiyar Sarkin Rano Ambassador Muhammad Isa Umaru a garin na Rano wacce ta rasu makonni biyu da suka gabata.

Da yake nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa jagorantar tawaga mai ƙarfi zuwa yi masa ta’aziyya.

Wakilin mu na gidan Gwamnatin kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa ‎Gwamna Abba ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan Hajiya maimuna, tare da sauran al’ummar musulmi baki daya.

 

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bukaci-sarakunan-jihar-domin-yin-adduoin-zaman-lafiya/feed/ 0 58592
‘Yan bindiga sun sace sakataren ƙaramar hukuma a Kano https://freedomradionig.com/yan-bindiga-sun-sace-sakataren-%c6%99aramar-hukuma-a-kano/ https://freedomradionig.com/yan-bindiga-sun-sace-sakataren-%c6%99aramar-hukuma-a-kano/#respond Sun, 22 Mar 2026 11:07:09 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58333 Wasu ƴanbindiga sun kai hari gidan sakataren ƙaramar hukumar Kibiya da ke jihar Kano tare da sace shi.

 

Shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Sabo Yusuf Usman ya shaida wa BBC cewa lamari ya faru ne ranar Juma’a da daddare a gidan sakataren da ke garin Dinya.

 

”Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da sakataren ke barci a gidansa”, in ji shi.

 

Ya ci gaba da cewa lokacin da maharan suka je gidan sun tashi ɗan gidan sakataren da ke kwana a zauren waje, inda suka tilasta masa ƙwanƙwasa kofar gidan, sannan ya faɗa wa mahaifinsa cewa cikinsa na ciwo.

 

”Hakan kuwa aka yi, bayan ya ƙwanƙwasa mahaifin nasa ya ce wane ne? Sai ya ce shi ne (ɗansa), ya ce me ya faru? Sai ya ce cikinsa ne ke ciwo, nan take mahaifin ya buɗe ƙofa, daga nan maharan suka kama shi tare da ɗan nasa”, a cewar Hon Sabo.

 

Ya ƙara da cewa tuni dai jamai’an tsaro suka kai taimakon gaggawa, amma kafin zuwansu maharan sun tafi da sakataren bayan sun sako ɗan nasa.

 

A baya dai ba a san ƙaramar hukumar Kibiya da matsalar tsaro ba, amma an sha samun matsalolin hare-haren ƴanbindiga a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da suka yi iyaka da jihar Katsina.

]]>
https://freedomradionig.com/yan-bindiga-sun-sace-sakataren-%c6%99aramar-hukuma-a-kano/feed/ 0 58333
Sarki Sunusi zai gudanar da hawan Sallah – Gwamnatin Kano https://freedomradionig.com/sarki-sunusi-zai-gudanar-da-hawan-sallah-gwamnatin-kano/ https://freedomradionig.com/sarki-sunusi-zai-gudanar-da-hawan-sallah-gwamnatin-kano/#respond Wed, 18 Mar 2026 14:56:57 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58320 Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da al’umma cewa ta samu sahihan bayanan sirri daga Majalisar Tsaro ta Jiha, da ke nuna cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin haddasa rikice-rikice da tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan Eid-el-Fitr (Sallah) da ke tafe.

 

A sanarwar da Kwaminan yada labarai Comr. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar ya ce gwamnatin ta jaddada cewa duk da ƙoƙarinta na kare da bunƙasa al’adun gargajiya na Kano, ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba.

 

Bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince da waɗannan tsare-tsare:

 

Hawan Idi: Za a gudanar da shi karkashin jagorancin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, daga filin Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka tsara, har zuwa Gidan Shettima, sannan a ƙare a Kofar Fatalwa ta Fadar Sarkin Kano.

 

Hawan Nasarawa: Za a gudanar da shi a wani salo na musamman, amma ba tare da hawa dawakai ba.

 

Hawan Daushe: An dakatar da shi a wannan lokaci, kuma za a mayar da shi zuwa wasu bukukuwan Sallah na gaba, in Allah ya yarda.

 

Hawan Fanisau da Hawan Dorayi: Su ma an dakatar da su na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

 

Gwamnatin ta umarci dukkan hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen sa ido, tare da tabbatar da bin waɗannan umarni, da kuma ɗaukar duk matakan doka don hana duk wani tashin hankali kafin, lokacin, da bayan Sallah.

 

Haka kuma, gwamnati ta buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka, su ba hukumomin tsaro haɗin kai, su guji yaɗa jita-jita, tare da gudanar da harkokinsu cikin lumana a duk lokacin bukukuwan Sallah.

 

Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki don ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

 

A ƙarshe, gwamnati ta taya dukkan Musulmi murnar zagayowar Eid-el-Fitr, tare da fatan a yi Sallah lafiya.

]]>
https://freedomradionig.com/sarki-sunusi-zai-gudanar-da-hawan-sallah-gwamnatin-kano/feed/ 0 58320