Addini – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com ...Muryar Jama'a Tue, 02 Jun 2026 08:00:31 +0000 en-GB hourly 1 https://i0.wp.com/freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Freedom-Kano-e1568718728160.png?fit=32%2C32&ssl=1 Addini – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com 32 32 166714237 NAHCON zata fara dawo da Al’hazan Najeriya a gobe laraba https://freedomradionig.com/nahcon-zata-fara-dawo-da-alhazan-najeriya-a-gobe-laraba/ https://freedomradionig.com/nahcon-zata-fara-dawo-da-alhazan-najeriya-a-gobe-laraba/#respond Tue, 02 Jun 2026 08:00:31 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59242 Hukumar kula d aikin hajji ta kasa  NAHCON ta ce za a fara jigilar mahajjatan kasar nan  daga gobe Laraba.

Shugaban Sashen Kula da Jiragen Sama na NAHCON, Alhaji Habib Bello, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Makkah.

Bello ya ce kamfanonin jiragen sama ne suka tantance jadawalin tashi kuma Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta amince da  hakan.

A cewarsa,  jirin Max Air zai  fara jigilar dawowa a ranar 3 ga watan Yuni tare da mahajjata daga jihar Nasarawa, yayin da Flynas da Air Peace za su fara aiki a ranar 4 ga watan Yuni tare da mahajjata daga jihohin Ogun da Oyo. 

]]>
https://freedomradionig.com/nahcon-zata-fara-dawo-da-alhazan-najeriya-a-gobe-laraba/feed/ 0 59242
Gwamnatin Najeriya na nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci – MURIC https://freedomradionig.com/gwamnatin-najeriya-na-nuna-fifiko-tsakanin-musulmai-da-kiristoci-muric/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-najeriya-na-nuna-fifiko-tsakanin-musulmai-da-kiristoci-muric/#respond Sat, 02 May 2026 19:37:49 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58887 Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnatin Najeriya da nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci a ƙasar.

 

MURIC ta yi wannan kiran ne bayan ta samu rahotannin cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar gina wani katafaren coci da za kashe wa naira biliyan 25 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

 

A wata sanarwa da MURIC ta aike wa BBC, shugaban ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya kuma nuna takaici kan yadda gwamnatin ta tallafa wa waɗanda rikici ya shafa a jihar Filato da naira biliyan 2, ba tare da ta yi irin hakan a jihohin Sakkwato, Borno, Kebbi da Zamfara ba, da su ma suke fama da matsalolin tsaro.

 

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da ya sa ake nuna wannan fifiko. Musulmai a Najeriya ba su cancanci haka ba…,” in ji sanarwar.

 

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin Najeriyar ta ware irin waɗannan kuɗaɗe na kimanin naira biliyan 25, da kuma fili ga Musulman ƙasar domin su ma su gina katafaren masallaci a filin jirgin.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan haƙƙin mu ne. Kuma ya kamata a ba mu.”

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-najeriya-na-nuna-fifiko-tsakanin-musulmai-da-kiristoci-muric/feed/ 0 58887
Shugaban NAHCON ya musanta bada umarnin kama Editan News Point https://freedomradionig.com/shugaban-nahcon-ya-musanta-bada-umarnin-kama-editan-news-point/ https://freedomradionig.com/shugaban-nahcon-ya-musanta-bada-umarnin-kama-editan-news-point/#respond Wed, 22 Oct 2025 06:23:52 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56179 Shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya musanta zargin da jaridar News Point Nigeria ta wallafa cewa ya umarci jami’an tsaro su kama Editan ta.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai Ahmad Muazu, ya fitar a daren Talatar makon nan.

Sanarwar ta ce, labarin da aka wallafa, an kirkire shi ne domin bata sunan Farfesa Pakistan da kuma zubar da martabar hukumar da idon duniya.

]]>
https://freedomradionig.com/shugaban-nahcon-ya-musanta-bada-umarnin-kama-editan-news-point/feed/ 0 56179
NAHCON ta koka bisa rage wa Najeriya yawan kujerun Hajji https://freedomradionig.com/nahcon-ta-koka-bisa-rage-wa-najeriya-yawan-kujerun-hajji/ https://freedomradionig.com/nahcon-ta-koka-bisa-rage-wa-najeriya-yawan-kujerun-hajji/#respond Fri, 17 Oct 2025 13:18:52 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56073 Hukumar Jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta bayyana damuwa kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.

NAHCON ta yi gargaɗiin cewa matakin zai hana mutane da dama zuwa aikin Hajjin a shekara mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da Yawun Hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce hukumomin Saudiyya sun sanar da NAHCON cewa wuraren kwanan mutum 66,910 kawai aka keɓe wa ƙasar, wani abu da ke nuna adadin maniyyatan da aka ware wa Najeriyar.

Hukumar ta NAHCON ta ce hukumomin Saudiyyar sun ɗauki matakin ne saboda Najeria ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025.

Matakin na Saudiyyar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa , Bola Tinubu ya umarci hukumar NAHCON ta rage kuɗin aikin hajjin 2026.

]]>
https://freedomradionig.com/nahcon-ta-koka-bisa-rage-wa-najeriya-yawan-kujerun-hajji/feed/ 0 56073
Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-dakatar-da-malam-lawan-triumph-daga-yin-waazi/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-dakatar-da-malam-lawan-triumph-daga-yin-waazi/#respond Wed, 01 Oct 2025 15:03:50 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55689 Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma’aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-dakatar-da-malam-lawan-triumph-daga-yin-waazi/feed/ 0 55689
Gwamnatin Kano ta ce zata ɗauki matakin Shari’a kan zargin Malam Lawan Triumph na ɓatanci a cikin wani karatu da yayi. https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ce-zata-%c9%97auki-matakin-sharia-kan-zargin-da-ake-yi-wa-malam-lawan-triumph-na-%c9%93atanci-a-cikin-wani-karatu-da-yayi/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ce-zata-%c9%97auki-matakin-sharia-kan-zargin-da-ake-yi-wa-malam-lawan-triumph-na-%c9%93atanci-a-cikin-wani-karatu-da-yayi/#respond Wed, 24 Sep 2025 15:08:38 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55552 Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ɗauki mataki dai-dai da abin da shari’a ta tanadar kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Triumph na ɓatanci a cikin wani karatu da yayi.

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin wata zanga-zangar lumana da matasa suka gudanar tare da kawo ƙorafi a fadar gidan gwamnatin Kano.

A cewar gwamnan Abba kabir Yusuf gwamnati ba zata yi watsi da kowanne irin zargi da al’umma suka gabatar ba, musamman idan ya shafi cin mutunci ko rashin mutunta ɗabi’un addini da al’ada, inda Ya ce gwamnati zata tabbatar da adalci ta hanyar bin dokoki da ka’idojin da suka dace.

Da suke jawabi Matasan da suka gudanar da zanga-zangar da suka fito daga sassa daban-daban na Kano sun nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira kalaman batanci na Malam Lawan Triumph, inda Suka roƙi gwamnati ta dauki matakin da zai zama darasi ga kowa wajen kaucewa kalaman da ka iya tunzura jama’a.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-ce-zata-%c9%97auki-matakin-sharia-kan-zargin-da-ake-yi-wa-malam-lawan-triumph-na-%c9%93atanci-a-cikin-wani-karatu-da-yayi/feed/ 0 55552
Kano: Hukumar Shari’a ta ƙaddamar da kwamitoci 80 https://freedomradionig.com/kano-hukumar-sharia-ta-%c6%99addamar-da-kwamitoci-80/ https://freedomradionig.com/kano-hukumar-sharia-ta-%c6%99addamar-da-kwamitoci-80/#respond Tue, 09 Sep 2025 10:01:48 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55233 Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta ƙaddamar da kwamitoci guda Takwas, na malamai waɗanda za su rinƙa ziyartar hukumomi da makarantu da kuma kasuwanni, da sauran wurare, domin faɗakar da al’umma a ɓangarori daban-daban.

 

Kwamitocin sun haɗar da kwamitin da zai rinƙa zuwa hedikwatar Ƴan sandan Kano, da na Kasuwanni, da makarantu, da kuma na tashoshin Mota, da gidajen gyaran hali, da dai sauransu, domin faɗakar da al’umma, da ma mazauna gidaje, da makarantun.

 

Shugaban hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitocin a jiya Litinin a ofishin hukumar, inda ya ce kafa kwamitocin ya biyo bayan yadda suka lura da buƙatar hakan, bisa  ziyarar da hukumar ta kai hukumomi da kuma gidajen a baya, inda shugabannin wuraren suka bukaci hakan domin faɗakarwa, da ilimantar da al’umma.

 

Sheikh Abbas Daneji, ya kuma buƙaci kwamitocin da su tsaya tsayin daka wajen gudanar da aiki yadda ya kamata, domin faɗakar da al’umma, da wa’azantar wa, tare da gyaran tarbiyya a matakai daban-daban.

]]>
https://freedomradionig.com/kano-hukumar-sharia-ta-%c6%99addamar-da-kwamitoci-80/feed/ 0 55233
Gwamna Radda ya kaddamar da taron addu’o’i kan matsalolin tsaro https://freedomradionig.com/gwamna-radda-ya-kaddamar-da-taron-adduoi-kan-matsalolin-tsaro/ https://freedomradionig.com/gwamna-radda-ya-kaddamar-da-taron-adduoi-kan-matsalolin-tsaro/#respond Fri, 05 Sep 2025 09:04:23 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55167 Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin addu’o’i na musamman tare da malamai da shugabannin addini da masu rike da sarautun gargajiya domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

 

Wata sanarwra da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ce ta bayyana hakan.

 

Sanarwar ta ce, taron ya haɗa malamai da shugabannin al’umma da jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na jihar, inda aka gudanar da addu’o’i ga waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon matsalar tsaro tare da roƙon Allah ya ci gaba da bai wa jihar kariya daga matsalolin tsaro.

 

Gwamna Radda ya ce, matsalar tsaro ba ta da alaƙa da addini ko siyasa, inda ya jaddada cewa haɗin kai da hakuri su ne ginshiƙai wajen magance ta.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamna-radda-ya-kaddamar-da-taron-adduoi-kan-matsalolin-tsaro/feed/ 0 55167
Gwamnatin Kano ta sanar da Alhamis a matsayin ranar hutun shekarar Musulunci https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-sanar-da-alhamis-a-matsayin-ranar-hutun-shekarar-musulunci/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-sanar-da-alhamis-a-matsayin-ranar-hutun-shekarar-musulunci/#respond Wed, 25 Jun 2025 19:03:19 +0000 https://freedomradionig.com/?p=54301 Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis 26 ga watan Yunin bana a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan hijira.

 

Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yammacin yau Laraba.

 

Sanarwar, ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekara da ta fara da watan Muharram, wata na farko a kalandar Musulunci.

 

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da al’ummar Musulmi da su yi nazari bisa ayyukan da suka yi a shekarar da ta kare, sannan su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

Haka kuma, ta cikin sanarwar, gwamnan, ya tabbatar wa al’ummar jihar kudurin gwamnatinsa na inganta rayuwar su ta hanyar gudanar da sadaukarwa da kuma tsarin ci gaban al’umma.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-sanar-da-alhamis-a-matsayin-ranar-hutun-shekarar-musulunci/feed/ 0 54301
Gwamna Abba Kabir ya ziyarci Alhazan Kano a Saudiyya https://freedomradionig.com/gwamna-abba-kabir-ya-ziyarci-alhazan-kano-a-saudiyya/ https://freedomradionig.com/gwamna-abba-kabir-ya-ziyarci-alhazan-kano-a-saudiyya/#respond Sun, 08 Jun 2025 14:56:46 +0000 https://freedomradionig.com/?p=54115 Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar Sallah ga Alhazan jihar a masaukinsu da ke kasar Saudiyya, inda ya bai wa kowane mahajjaci kyautar Riyal 250, kwatankwacin Naira 105,000.

Gwamnan ya kai ziyarar ne a daren ranar Asabar.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba da nasarar aikin Hajjin bana da aka samu, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya fi na shekarun baya, musamman na bara.

Gwamnan ya bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa alaka da yin addu’o’i ga jihar Kano da Najeriya, da kuma mika gaisuwa ga mahajjata a bikin Sallah.

Ya kuma ce, Kano da Najeriya ma suna bukatar addu’a, don haka ya nemi Alhazan da su yi addu’o’i na musamman.

Gwamnan ya jajanta wa iyalan mahajjatan da suka rasa rayukansu a Makkah da Madina, da kuma lokacin Arafah, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan da wadanda suka rasu.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamna-abba-kabir-ya-ziyarci-alhazan-kano-a-saudiyya/feed/ 0 54115