Auwal Hassan Fagge – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com ...Muryar Jama'a Tue, 16 Jun 2026 20:22:26 +0000 en-GB hourly 1 https://i0.wp.com/freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Freedom-Kano-e1568718728160.png?fit=32%2C32&ssl=1 Auwal Hassan Fagge – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com 32 32 166714237 Majalisar Wakilai ta fara nazarin ƙudurorin sake fasalin rundunar soji https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-fara-nazarin-%c6%99udurorin-sake-fasalin-rundunar-soji/ https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-fara-nazarin-%c6%99udurorin-sake-fasalin-rundunar-soji/#respond Tue, 16 Jun 2026 15:37:15 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59519 Majalisar Wakilan Najeriya ta fara nazarin jerin ƙudurorin dokoki da ke da nufin sake fasalin tsarin rundunar soji da inganta walwalar jami’ai da tsofaffin sojoji, tare da ƙarfafa ƙarfin rundunar wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro.

 

Da yake jawabi a taron sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu da Kwamitin Tsaro na Majalisar ya shirya a Abuja, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce kudurorin na da muhimmanci wajen daidaita dokokin soja da sauye-sauyen da ke faruwa a fannin tsaro.

 

Ya bayyana cewa sabbin ƙalubalen tsaro da suka haɗa da fashin teku a yankin Gulf of Guinea, yaƙin yanar gizo da kuma haɗin gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata manyan laifuka sun nuna buƙatar yin garambawul ga dokokin rundunar sojin Najeriya.

 

Daga cikin muhimman kudurorin da ake dubawa akwai kudirin Armed Forces Farms and Ranches Scheme Bill, wanda ke da nufin haɗa shirye-shiryen samar da abinci da ayyukan soja, musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

 

A nasa jawabin, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Babajimi Benson, ya ce taron wata muhimmiyar dama ce ga masu ruwa da tsaki su taimaka wajen tsara dokokin da za su ƙarfafa tsaro, ilimin soja, bincike, kula da lafiya, walwalar tsofaffin sojoji, samar da abinci da kuma daidaito a rundunar sojin kasar.

]]>
https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-fara-nazarin-%c6%99udurorin-sake-fasalin-rundunar-soji/feed/ 0 59519
Gwamna Abba ya taya Musulmi murnar shiga shekarar 1448 https://freedomradionig.com/gwamna-abba-ya-taya-musulmi-murnar-shiga-shekarar-1448/ https://freedomradionig.com/gwamna-abba-ya-taya-musulmi-murnar-shiga-shekarar-1448/#respond Tue, 16 Jun 2026 14:07:13 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59512 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar Musulmi na Kano da ma Najeriya baki ɗaya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan Hijira.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Ta cikin sanarwar, ya ce, gwamnan ya bayyana cewa sabuwar shekarar Musulunci wata dama ce ta yin tunani kan darussan Hijirar Annabi Muhammad (SAW), musamman game da haƙuri, sadaukarwa, jajircewa da cikakken dogaro ga Allah.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Hijirar Annabi daga Makkah zuwa Madina ba tafiya ce kawai ba, illa wani babban sauyi da ya kafa tubalin al’umma mai adalci, tausayi da haɗin kai.

Sanarwa ta kara da cewa Gwamnan, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da rungumar kyawawan ɗabi’u da za su inganta zaman lafiya, haƙuri da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yau na buƙatar jama’a su yi koyi da darussan Hijira ta hanyar guje wa rarrabuwar kawuna, ƙiyayya da son kai, tare da rungumar haɗin kai da aiki tare domin ci gaban al’umma.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamna-abba-ya-taya-musulmi-murnar-shiga-shekarar-1448/feed/ 0 59512
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kwamitin bincike kan zargin karkatar da abincin yara https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-%c6%99addamar-da-kwamitin-bincike-kan-zargin-karkatar-da-abincin-yara/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-%c6%99addamar-da-kwamitin-bincike-kan-zargin-karkatar-da-abincin-yara/#respond Tue, 16 Jun 2026 11:58:28 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59524 Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani kwamiti domin gudanar da bincike kan zargin karkatarwa da sace da kuma sayar da kayan abincin yara, wato Tamowa a fadin Jihar.

Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ƙaddamar da kwamitin.

A cewar kwamishinan an kafa kwamitin ne domin gano gaskiyar abin da ya faru dangane da zargin karkatar da kayayyakin da aka tanada domin ceton rayukan yara masu fama da cutar tamowa, tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Haka kuma, kwamitin zai tantance adadi da kuma kimar kayayyakin da suka bace, sannan ya bayar da shawarwari kan matakan hukunci da gyaran da ya dace, tare da gabatar da rahotonsa cikin kwanaki goma sha hudu daga ranar kaddamar da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira miliyan dari biyar wajen sayo wadannan kayayyaki domin kula da yara masu fama da cutar Tamowa.

Babban sakataren na ma’aikatar Aminu Bashir, ne zai jagoranci kwamitin, wanda ya kunshi mambobi goma sha takwas daga hukumomi da bangarori daban-daban da suka haɗa da jami’an tsaro, wakilan masarauta da masu unguwanni.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-%c6%99addamar-da-kwamitin-bincike-kan-zargin-karkatar-da-abincin-yara/feed/ 0 59524
Gwamnatin Kano na shirin dasa bishiyoyi guda 10,000 https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-na-shirin-dasa-bishiyoyi-guda-10000/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-na-shirin-dasa-bishiyoyi-guda-10000/#respond Tue, 16 Jun 2026 10:09:31 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59528 Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara karɓar buƙatun neman tsirran bishiyoyi a ƙarƙashin shirin dasa bishiyoyi miliyan 10, wanda ke da nufin yaƙi da hamada, farfaɗo da muhallin da ya lalace, da kuma rage illolin sauyin yanayi.

Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ƙungiyoyin ci gaban al’umma, ƙungiyoyin sa-kai, ƙungiyoyin matasa, makarantu da cibiyoyin addini na iya neman tsirran domin dasawa a yankunansu.

Ya ce shirin na ci gaba ne da yunƙurin gwamnati na kare muhalli, yana kuma daga cikin manyan tsare-tsaren jihar na tinkarar sauyin yanayi da farfaɗo da muhallin da ya lalace.

A cewarsa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bai wa ma’aikatar cikakken goyon baya domin aiwatar da shirye-shiryen da za su ƙara yawan bishiyoyi a fadin jihar.

Kwamishinan ya buƙaci ƙungiyoyin da ke da sha’awar shiga shirin su cike fom ɗin neman tsirran ta shafin da Gwamnatin ta samar

Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su rungumi wannan shiri a matsayin gudummawa wajen kare muhalli, yana mai cewa haɗin kan al’umma ne zai tabbatar da nasarar shirin dasa bishiyoyi miliyan 10 domin amfanin wannan ƙarni da waɗanda za su zo nan gaba.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-na-shirin-dasa-bishiyoyi-guda-10000/feed/ 0 59528
Kaduna: Ƴan Sanda sun kama mutane 12 da ake zargi da satar mutane https://freedomradionig.com/kaduna-%c6%b4an-sanda-sun-kama-mutane-12-da-ake-zargi-da-satar-mutane/ https://freedomradionig.com/kaduna-%c6%b4an-sanda-sun-kama-mutane-12-da-ake-zargi-da-satar-mutane/#respond Tue, 16 Jun 2026 09:16:53 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59534 Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutane 12 da ake zargi da garkuwa da mutane tare da kwato bindigogi kirar AK-47 da miyagun kwayoyi a jihar.

 

Hakan na cikin bayanin da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansur Hassan, ya fitar a yau Talata.

Ya ce rundunar ta samu nasarar kama mutane 12 da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.

 

Mansur Hassan ya ce jami’an rundunar sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 da kwayoyin Tramadol guda 2,700.

 

Ya kara da cewa an kwato motoci guda hudu a yayin aikin da jami’an tsaron suka gudanar.

]]>
https://freedomradionig.com/kaduna-%c6%b4an-sanda-sun-kama-mutane-12-da-ake-zargi-da-satar-mutane/feed/ 0 59534
Gwamnatin Katsina ta sanya dokoki a kan Fetur da POS da cajin waya a Matazu da Musawa https://freedomradionig.com/gwamnatin-katsina-ta-sanya-dokoki-a-kan-fetur-da-pos-da-cajin-waya-a-matazu-da-musawa/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-katsina-ta-sanya-dokoki-a-kan-fetur-da-pos-da-cajin-waya-a-matazu-da-musawa/#respond Tue, 16 Jun 2026 08:07:18 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59532 Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta saye, sayarwa, jigila da ajiye man fetur a jarkoki a fadin jihar tare da rufe sana’ar POS da wuraren cajin waya a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa.

 

Hakan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a Daren jiya Litinin.

 

Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya amince da sabbin matakan bayan wani taron gaggawa kan tsaro da ya hada hukumomin tsaro, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Ya kara da cewar an dauki matakan ne domin dakile ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, bayan binciken tsaro ya nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da man fetur, POS da wuraren cajin waya wajen gudanar da ta’ asar su

 

Gwamnatin jihar ta kuma haramta amfani da babura a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa domin rage zirga-zirgar masu aikata laifuka a yankunan.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-katsina-ta-sanya-dokoki-a-kan-fetur-da-pos-da-cajin-waya-a-matazu-da-musawa/feed/ 0 59532
Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu Jam’iyyu 4 https://freedomradionig.com/kotu-ta-umarci-inec-ta-soke-rajistar-adc-da-wasu-jamiyyu-4/ https://freedomradionig.com/kotu-ta-umarci-inec-ta-soke-rajistar-adc-da-wasu-jamiyyu-4/#respond Mon, 15 Jun 2026 21:56:34 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59509 Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci hukumar zaɓe ta Najeriya INEC da ta soke rajistar jam’iyyu biyar da suka haɗa da African Democratic Congress ADC, bisa zargin gaza cika wasu sharuɗɗan da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada ga jam’iyyun siyasa.

 

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda ya ce jam’iyyun sun kasa samun akalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata.

 

Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, Accord A, Action Alliance AA, Action Peoples Party APP da Zenith Labour Party ZLP.

 

Kotun ta kuma umarci INEC da kada ta bari waɗannan jam’iyyu su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen shekarar 2027, matuƙar ba a samu sauyi a shari’ar ba.

 

Wata ƙungiya mai suna Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ce ta shigar da ƙarar, tana mai zargin jam’iyyun da gaza cika sharuddan da suka shafi yaɗuwar tasirin siyasa da kuma sakamakon zaɓe kamar yadda doka ta tanada.

 

Ƙungiyar ta buƙaci kotun da ta umarci soke rajistar jam’iyyun, tana mai cewa ba su gabatar da hujjojin da za su karya zarge-zargen da ake musu ba.

 

Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

]]>
https://freedomradionig.com/kotu-ta-umarci-inec-ta-soke-rajistar-adc-da-wasu-jamiyyu-4/feed/ 0 59509
NDC ta zaɓi Mustapha Kwankwaso a matsayin mataimakin gwamna https://freedomradionig.com/ndc-ta-za%c9%93i-mustapha-kwankwaso-a-matsayin-mataimakin-gwamna/ https://freedomradionig.com/ndc-ta-za%c9%93i-mustapha-kwankwaso-a-matsayin-mataimakin-gwamna/#respond Mon, 15 Jun 2026 19:07:18 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59506 Jam’iyyar NDC ta zabi Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin dan takarar mataimakin gwamnan Kano.

 

Shugaban kungiyar Kwankwasiyya Scholars Dr. Mansur Hassan Kumbotso ne ya tabbatar da labarin a zantawarsa da Freedom Radio.

]]>
https://freedomradionig.com/ndc-ta-za%c9%93i-mustapha-kwankwaso-a-matsayin-mataimakin-gwamna/feed/ 0 59506
Kano Pillars ta musanta wasu zarge-zarge da ake yaɗa wa kan ƙungiyar https://freedomradionig.com/kano-pillars-ta-musanta-wasu-zarge-zarge-da-ake-ya%c9%97a-wa-kan-%c6%99ungiyar/ https://freedomradionig.com/kano-pillars-ta-musanta-wasu-zarge-zarge-da-ake-ya%c9%97a-wa-kan-%c6%99ungiyar/#respond Mon, 15 Jun 2026 18:49:40 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59503 Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta musanta wasu zarge-zargen da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta dangane da jagororin tawagar.

A cewar ƙungiyar wasu marasa kishin jihar Kano da harkokin wasanni su ke ɗaukar nauyin yin hakan.

Ta cikin sanarwar da sashen yaɗa labarai na kungiyar ya fitar, Kano Pillars ta yi kira ga magoya bayan tawagar da su yi watsi da irin waɗannan kalami da ta kira da karairayi.

Haka kuma ta ƙara da cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin irin waɗannan labarai.

]]>
https://freedomradionig.com/kano-pillars-ta-musanta-wasu-zarge-zarge-da-ake-ya%c9%97a-wa-kan-%c6%99ungiyar/feed/ 0 59503
Gwamnatin Kano ta bayyana ranar Talata a matsayin hutun sabuwar shekara Musulunci https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bayyana-ranar-talata-a-matsayin-hutun-sabuwar-shekara-musulunci/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bayyana-ranar-talata-a-matsayin-hutun-sabuwar-shekara-musulunci/#respond Mon, 15 Jun 2026 17:02:27 +0000 https://freedomradionig.com/?p=59497 Gwamnatin Kano ta bayyana gobe Talata daya ga watan Muharram Hijira ta 1448 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata.

Hakan na cikin sanarwar da Daraktar ayyuka Hajiya Safiyya Ali Sulaiman ta fitar a madadin shugabar ma’aikata ta Kano

A cewar sanarwar bayar da hutun na zuwa ne sakamakon shigowar da watan musulunci zai yi daga gobe Talata 16 ga watan Yunin 2026 da muke ciki.

Ta cikin sanarwar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bukaci ma’aikatan da su yi amfani da hutun wajen yiwa Kano addu’oin zaman Lafiya da karuwar arziki mai dorewa.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-kano-ta-bayyana-ranar-talata-a-matsayin-hutun-sabuwar-shekara-musulunci/feed/ 0 59497