ilimi – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com ...Muryar Jama'a Sat, 18 Apr 2026 11:38:29 +0000 en-GB hourly 1 https://i0.wp.com/freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Freedom-Kano-e1568718728160.png?fit=32%2C32&ssl=1 ilimi – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com 32 32 166714237 Malaman makaranta a Abuja za su tsunduma yajin aiki https://freedomradionig.com/malaman-makaranta-a-abuja-za-su-tsunduma-yajin-aiki/ https://freedomradionig.com/malaman-makaranta-a-abuja-za-su-tsunduma-yajin-aiki/#respond Sat, 18 Apr 2026 11:38:29 +0000 https://freedomradionig.com/?p=58674 Reshen kungiyar malaman makaranta ta NUT na Abuja Babban Birnin Tarayyar Nijeriya ya umarci malaman makarantun firamare da sakandare a dukkan gundumomi shida da ke yankin da su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026.

 

Shugaban kungiyar Comr Abdullahi Mohammed Shafas, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na reshen jiha (SWEC) da aka gudanar a Teachers House da ke Gwagwalada.

 

Ya ce sun dauki matakin ne saboda rashin fitar da kuma aiwatar da rahoton da ya shafi hakkokin da malaman ke bi wanda gwamnatin FCT ta kasa kammalawa.

]]>
https://freedomradionig.com/malaman-makaranta-a-abuja-za-su-tsunduma-yajin-aiki/feed/ 0 58674
Sace daliban Kebbi hari ne kai tsaye ga makomar Najeriya- Ministar Mata https://freedomradionig.com/sa-ce-daliban-kebbi-hari-ne-kai-tsaye-ga-makomar-najeriya-ministar-mata/ https://freedomradionig.com/sa-ce-daliban-kebbi-hari-ne-kai-tsaye-ga-makomar-najeriya-ministar-mata/#respond Thu, 20 Nov 2025 07:50:26 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56733 Ministar harkokin Mata Imaan Sulaiman Ibrahim, ta nemi a gaggauta sakin dalibai mata 25 na jihar Kebbi da aka sace, ta na mai bayyana lamarin a matsayin hari kai tsaye ga makomar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ministar ta ce, sace daliban ba wai kawai cin zarafin iyayensu ba ne, har ma yana nuna irin barazanar da ‘yan ta’adda ke yi wa ilimi da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Ministar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara matsa kaimi wajen ceto yaran cikin koshin lafiya tare da tabbatar da cewa irin wannan ta’addanci bai sake faruwa ba a ko’ina.

]]>
https://freedomradionig.com/sa-ce-daliban-kebbi-hari-ne-kai-tsaye-ga-makomar-najeriya-ministar-mata/feed/ 0 56733
Majalisar Wakilai ta gargadi hukumar WAEC https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-gargadi-hukumar-waec/ https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-gargadi-hukumar-waec/#respond Fri, 14 Nov 2025 07:02:04 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56612 Majalisar Wakilan Najeriya, ta gargadi Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC kan shirin da ta ke yi na fara yin amfani da kwamfuta daga shekara da ke tafe ta 2026, tana mai cewa hakan na iya janyo yawan faduwar dalibai idan ba a shirya tsaf ba kafin aiwatar da sabon shirin.

Ɗaya daga cikin mambobin majalisar ya bayyana cewa, yawancin makarantu a sassan ƙasar nan basu da kayan aiki da kuma horo da zai bai wa ɗalibai damar yin irin wannan jarrabawa ta kwamfuta cikin sauƙi.

Majalisar ta bukaci WAEC da ma’aikatar ilimi ta ƙasa da su tsara hanyoyin horar da malamai da ɗalibai tun daga yanzu, domin kaucewa matsaloli.

]]>
https://freedomradionig.com/majalisar-wakilai-ta-gargadi-hukumar-waec/feed/ 0 56612
An fara gudanar da taron KANSIS25 https://freedomradionig.com/an-fara-gudanar-da-taron-kansis25/ https://freedomradionig.com/an-fara-gudanar-da-taron-kansis25/#respond Wed, 22 Oct 2025 10:21:35 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56186 An fara gudanar da taron Kano Social Influencers Summit na bana wanda cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban Al’umma CITAD ke gudanarwa duk shekara karo na 6 watau KANSIS25.

Taron na KANSIS, wanda CITAD ta fara gudanarwa tun a shekarar 2019, ya na haɗa masana da dama daga sassa daban-daban na Najeriya inda ake tattaunawa musamman kan amfani da fasahar zamani wajen samar da ayyukan ci gaban al’umma.

Kamar yadda aka saba ana gudanar da taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda na bana za a gudanar da shi a tsakanin yau Laraba da kuma gobe Alhamis a jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u da ke tsakiyar birnin Kano.

Haka kuma, taron na bana, zai mayar da hankali ne wajen ɗabbaka tsarin yin amfani da fasahar zamani mai amfani da tinanin Ɗan-adam watau AI.

]]>
https://freedomradionig.com/an-fara-gudanar-da-taron-kansis25/feed/ 0 56186
ASUU ta koka kan jinkirin naɗa shugaban Jami’ar Northwest https://freedomradionig.com/asuu-ta-koka-kan-jinkirin-na%c9%97a-shugaban-jamiar-northwest/ https://freedomradionig.com/asuu-ta-koka-kan-jinkirin-na%c9%97a-shugaban-jamiar-northwest/#respond Mon, 20 Oct 2025 20:34:57 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56140 Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU, reshen Jami’ar Northwest da ke nan Kano, ta bayyana damuwarta kan jinkirin da aka samu wajen samar da sabon Shugaban jami’ar watau  Vice Chancellor na dindindin.

ASUU, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a Litinin ɗin makon nan mai ɗauke da sa hannun shugabanta na  reshen jami’ar ta Northwest Kwamared Mansur Sa’id, da Sakatarenta Kwamared Yusuf Ahmad Gwarzo, inda ta bayyana cewa wannan jinkiri ka iya haifar da matsaloli wajen gudanar da harkokin jami’ar.

Haka kuma ta cikin sanarwar, Kungiyar ta ce wa’adin tsohon shugaban Jami’ar ya ƙare ne a ranar 15 ga watan nan da muke ciki na Oktoban bana, kuma tun daga lokacin Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Harkokin Karatu ne ke rike da mukamin shugaban rikon kwarya, inda ASUU ta ce wannan tsarin ba ya cikin dokar kafa Jami’ar Northwest ta shekarar 2012 wadda aka yi wa kwaskwarima.

ASUU ta jaddada cewa, bisa tanadin sashen 9 (2) na dokar jami’ar, nadin Shugaban Jami’a ya rataya ne a kan Hukumar Gudanarwa tare da tabbatarwa daga Mai Ziyarar Jami’ar, tare da cewa, dokar ta fayyace yadda za a gudanar da aikin tantancewa da nada wanda zai rike mukamin, wanda ya haɗa da ayyana kujerar a matsayin wadda babu mai ita, sannan a kafa kwamitin bincike da kuma miƙa sunan mutane 3 da aka zaba zuwa ga Majalisar gudanarwa domin tabbatar da guda daga cikinsu.

Kungiyar ta ce tana bibiyar lamuran da suka shafi nadin, inda ta tabbatar cewa Hukumar Gudanarwa ta kammala aikin ta har zuwa matakin zaben wanda ya dace da mukamin, a taro na musamman da aka gudanar ranar 2 ga Oktoba, 2025.

Sai dai ASUU ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda Hukumar ba ta sanar da sakamakon taron ga ma’aikatan jami’ar ba, kuma ba ta miƙa sunan wanda aka zaɓa domin tabbatarwa ba.

ASUU ta yi gargadin cewa jinkirin ya na iya zama saba wa doka, tana kuma kira da a gaggauta ɗaukar mataki domin kauce wa haifar da tsaiko a harkokin gudanarwa da tsarin shugabanci.

Kungiyar ta kuma bukaci a bi ƙa’idar da doka ta tanada, ba tare da tsoma baki daga kowanne ɓangare ba.

A cewar ASUU shiyyar ta jami’ar Northwest, jinkirin tabbatar da sabon shugaban jami’ar na iya haifar da rashin tabbas a shugabanci da kuma tasiri ga ci gaban karatu da gudanarwa.

Kungiyar ta tabbatar da aniyar ta na kare mutuncin tsarin jami’o’i tare da tabbatar da bin ƙa’ida da gaskiya a duk harkokin gudanarwa na jami’ar.

]]>
https://freedomradionig.com/asuu-ta-koka-kan-jinkirin-na%c9%97a-shugaban-jamiar-northwest/feed/ 0 56140
Muna ci gaba da tattaunawa da wakilan Gwamnatin Tarayya- ASUU https://freedomradionig.com/muna-ci-gaba-da-tattaunawa-da-wakilan-gwamnatin-tarayya-asuu/ https://freedomradionig.com/muna-ci-gaba-da-tattaunawa-da-wakilan-gwamnatin-tarayya-asuu/#respond Mon, 20 Oct 2025 07:58:47 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56121 Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU, ta tabbatar da cewa ta na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya da Alhaji Yayale Ahmed ke jagoranta, yayin da yajin aikin gargadin na mako biyu da ASUU din ke yi yanzu haka ya shiga rana ta bakwai.

 

Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa Farfesa Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa, an samu ci gaba a bangarori biyar daga cikin bukatun su guda bakwai da suka hada da biyan hakkokin su da suke bin gwamnati ba shi. 

 

Ya kuma bayyana cewa, an samu shiga tsakani daga wasu fitattun ’yan kasa don kawo karshen rikicin. ASUU ta bukaci mambobinta da su ci gaba da kasancewa masu juriya da hadin kai, tare da bin umarnin shugabannin rassan su. Yajin aikin dai yana da nufin matsa wa gwamnati lamba kan aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla dan inganta walwalar malamai da harkar ilimi. 

 

Idan ba a manta ba a ranar Litinin din da ta gabata 13 ga wannan wata. Kungiyar ta Asuu ta nasar da tsunduma yajin aiki gargadi na makwanni 2.

]]>
https://freedomradionig.com/muna-ci-gaba-da-tattaunawa-da-wakilan-gwamnatin-tarayya-asuu/feed/ 0 56121
Gwamnatin tarayya ta ce haryanzu darussan Lissafi da Turanci wajibi ne ga dalibai masu shirin shiga manyan makarantu https://freedomradionig.com/gwamnatin-tarayya-ta-ce-haryanzu-darussan-lissafi-da-turanci-wajibi-ne-ga-dalibai-masu-shirin-shiga-manyan-makarantu/ https://freedomradionig.com/gwamnatin-tarayya-ta-ce-haryanzu-darussan-lissafi-da-turanci-wajibi-ne-ga-dalibai-masu-shirin-shiga-manyan-makarantu/#respond Sun, 19 Oct 2025 20:34:10 +0000 https://freedomradionig.com/?p=56115  

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Turanci da Lissafi sun ci gaba da zama dole a O’Level

 

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar yada Labarai da hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a Abuja ranar Lahadi.

 

Ta ce an fitar da wannan bayani ne domin fayyace rashin fahimta da ya biyo bayan sabon tsarin da aka sanar na sauƙaƙe sharuddan karɓar ɗalibai a jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.

]]>
https://freedomradionig.com/gwamnatin-tarayya-ta-ce-haryanzu-darussan-lissafi-da-turanci-wajibi-ne-ga-dalibai-masu-shirin-shiga-manyan-makarantu/feed/ 0 56115
CONUA ta barranta kanta da yajin aikin ASUU https://freedomradionig.com/conua-ta-barranta-kanta-da-yajin-aikin-asuu/ https://freedomradionig.com/conua-ta-barranta-kanta-da-yajin-aikin-asuu/#respond Mon, 13 Oct 2025 11:29:04 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55975 Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa CONUA ta ce bata cikin yajin aikin da aka fara yau na jami’o’in Najeriya.

 

Shugaban ƙungiyar na kasa, Dakta Niyi Sunmonu ne ya tabbatar da haka,  a wata sanarwa da ya fitar, ga manema labarai.

A cikin sanarwar Dakta Niyi ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa kungiyar ta CONUA ta shiga yajin aikin da ASUU ta fara a yau Litinin.

Ya kuma bayyana cewa, zuwa yanzu,  kungiyar ba ta ayyana wani yajin aiki ba, tana kuma jajircewa wajen ganin tsarin jami’o’i ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ta hanyar tattaunawa da gwamnati cikin lumana.

Sunmonu ya bukaci mambobin kungiyar da su ci gaba da zuwa aikin koyarwa da kuma kula da dalibai kamar yadda aka saba, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jami’o’i.

 

]]>
https://freedomradionig.com/conua-ta-barranta-kanta-da-yajin-aikin-asuu/feed/ 0 55975
Za mu sama wa malamai fiye da 2,000 filaye- ASUSS https://freedomradionig.com/za-mu-sama-wa-malamai-fiye-da-2000-filaye-asuss/ https://freedomradionig.com/za-mu-sama-wa-malamai-fiye-da-2000-filaye-asuss/#respond Mon, 06 Oct 2025 07:05:02 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55763 Kungiyar Malaman makarantun sakandare ASUSS shiyyar Kano, ta ce za ta samar da filaye fiye da guda Dubu Biyu ga mambobinta a kokarinta na saukaka wa malamai wajen mallakar muhalli.

 

Shugaban kungiyar Kwamared Abdu Usman Yalo, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da freedom Radio a wani bangare bikin ranar Malamai ta duniya.

 

Kwamared Abdu Yalo ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kano da ta sanya wa Malamai alawus karshen kowanne wata domin kara inganta ayyukansu.

]]>
https://freedomradionig.com/za-mu-sama-wa-malamai-fiye-da-2000-filaye-asuss/feed/ 0 55763
Za mu dauki nauyin karatun duk mahaddacin da ke shirin yin karatun Boko- Gwamna Radda https://freedomradionig.com/za-mu-dauki-nauyin-karatun-duk-mahaddacin-da-ke-shirin-yin-karatun-boko-gwamna-radda/ https://freedomradionig.com/za-mu-dauki-nauyin-karatun-duk-mahaddacin-da-ke-shirin-yin-karatun-boko-gwamna-radda/#respond Tue, 23 Sep 2025 14:23:22 +0000 https://freedomradionig.com/?p=55528 Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce, gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun duk wanda ya haddace Alƙur’ani kuma ya ke son ci gaba da ilimi a fannonin zamani kamar likitanci ko unguwanzoma da sauran fannonin ayyukan zamani.

Gwamnan ya bayyana haka ne a babban taron da aka gudanar domin gyara tsarin karatun Almajiri da Islamiyya a jihar, inda malamai, shugabannin al’umma, ƙungiyoyi da hukumomi suka halarta.

Radda ya ce, gwamnati za ta kafa sabbin makarantu guda uku da za su haɗa mahaddata Alƙur’ani da ilimin zamani irin su Turanci, Lissafi da koyon sana’o’in hannu ga yara maza da mata.

Ya kuma jaddada cewa malamai za su taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar wannan shirin, in da ya bukaci   iyaye da al’umma da su bayar da goyon baya domin gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalar almajiranci ba.

Rahotonni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata.

]]>
https://freedomradionig.com/za-mu-dauki-nauyin-karatun-duk-mahaddacin-da-ke-shirin-yin-karatun-boko-gwamna-radda/feed/ 0 55528