FRNigeria – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com ...Muryar Jama'a Fri, 08 Mar 2024 06:21:32 +0000 en-GB hourly 1 https://i0.wp.com/freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/09/Freedom-Kano-e1568718728160.png?fit=32%2C32&ssl=1 FRNigeria – Freedom Radio Nigeria https://freedomradionig.com 32 32 166714237 Za mu ƙirƙiro hanyoyin da zasu inganta harkar Noma da kiwo-MD KNARDA https://freedomradionig.com/za-mu-%c6%99ir%c6%99iro-hanyoyin-da-zasu-inganta-harkar-noma-da-kiwo-md-knarda/ https://freedomradionig.com/za-mu-%c6%99ir%c6%99iro-hanyoyin-da-zasu-inganta-harkar-noma-da-kiwo-md-knarda/#respond Fri, 08 Mar 2024 05:47:50 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51873 Gwamnatin jihar Kano ta ce lokacin da ta karɓi gwamnati ta sami hukumar bunƙasa noma da raya karkara ta Knarda a cikin mawuyacin halin, kasan cewar yadda ma’aikatan hukumar basa son zuwa aiki,

Sai dai kawo wannan lokacin hukumar ta fito da hanyoyin gyara domin farfaɗo da hukumar, inda yanzu haka aka cimma nasara wajen daukar saitin ma’aikata.

Shugaban hukumar Dakta Farouk Kurawa ne yayi wannan jawabin yayin da yake ganawa da manema labarai kan irin kalubalen da hukumar take ciki kafin karɓar sa da kuma irin nasarar da suka samu zuwa yanzu.

Haka zalika Dakta Farouk Kurawa ya ce wannan hukumar tana kula da yadda za’a gudanar noma da bayar da horo ga malan gona, yadda ya kamata domin samin anfanin gona a faɗin jihar kano dama ƙasa baki ɗaya.

Kurawa ya ce yanzu haka suna tuntubar hukumomi daban daban na gwamnatin tarayya domin bayar da tallafi ga jihar kano wanda zai anfani jihar da manoma baki ɗaya.

Haka kuma yanzu haka muna haɗa ƙididdigar manoman da suke jihar Kano domin tabbatar da kasafi akan harkar noma.

Mun ɓuƙaci gwamnatin tarayya ta ware kudi kaso 70 cikin ɗari wajen inganta harkokin malaman gona wanda haka zai inganta harkar noma a faɗin ƙasar nan A cewar Kurawa.

Akwai hukumomi da suke gudanar da ayyuka, mun shiga aiki da su domin koyar da mata sana’o’in daban daban na noma da sarrafa anfanin gona wanda ya shafi gyada,masara da dai sauran kayan anfanin gona.

Akwai tsarin bayar da kayan kiyo ga mata a faɗin jihar Kano wanda yanzu haka wannan tsari yayi nisa a faɗin jihar domin samar da kayan kiwo a faɗin jihar Kano. haka zalika wannan shirin zai samar da mayanka a dukkanin kananan hukumomi na Kano domin tsaftace harkar yanka dabbobi.

Yanzu haka akwai shirin tallafawa manoma da taki iri daban-daban domin samar da anfanin gona mai kyau a faɗin jihar Kano.

Kurawa yace yanzu haka akwai tsarin gyara hanyoyi a kasuwar hatsi ta Dawanau domin samin saukin zirga-zirga ababan hawa musamman masu dauko kayan hatsi.

Haka kuma zamu ci gaba da shigo da tsare-tsare wanda zai ƙara haɓakar harkar noma da kiwo a faɗin jihar Kano.

]]>
https://freedomradionig.com/za-mu-%c6%99ir%c6%99iro-hanyoyin-da-zasu-inganta-harkar-noma-da-kiwo-md-knarda/feed/ 0 51873
Za mu tabbatar ruwan fanfo ya isa ko ina a Kano- MD https://freedomradionig.com/za-mu-tabbatar-ruwan-fanfo-ya-isa-ko-ina-a-kano-md/ https://freedomradionig.com/za-mu-tabbatar-ruwan-fanfo-ya-isa-ko-ina-a-kano-md/#respond Wed, 06 Mar 2024 16:36:31 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51859 Zamu tabbatar ruwan fanfo ya isa ko ina a faɗin Kan.

Shugaban ma’aikatan jihar Kano Alh.Abdullahi Musa ya yi kira ga ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta jihar Kano da su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu.

Alhaji Abdullahi Musa ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda aikin su yake wakana domin ƙara karfafa musu gwiwa.

Haka zalika shugaban ma’aikatan ya yabawa Manajan Daraktan hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi kan samar da ruwan sha ga sakatariyar Audu Bako cikin kankanin lokaci inda ya jaddada bukatar hukumar ta yi aiki tare da samar da wasu tsare-tsare na inganta samar da ruwan sha a jihar.

A nasa bangaren Manajan Daraktan Injiniya Garba Ahmad Bichi ya yi alkawarin sake rubanya ƙoƙarin samar da isasshen ruwa ga al’umma.

Injiniya Garba Bichi ya godewa shugaban ma’aikatan bisa wannan ziyarar da ya kawo masa tare da yi masa fatan alheri.

A wani labarin kuma Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano Injiniya Garba Ahmad Bichi ya jaddada kudirin sa na tabbatar da samar da ruwan sha a jihar.

Injiniya Garba Bichi ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jami’ar Yusif Maitama Sule a ofishinsa Ya yi alkawarin gyara matsalar da ke hana zuwan ruwa a sabon Jami’ar inda ya nuna godiya ga mahukuntan makarantar da suka kai rahoto ga hukumar.

Da yake jawabi tun da farko Farfesa Abubakar Salisu ya ce sun je ofishin MD ne domin neman taimakon hukumar ta samar da ruwan sha a jami’ar.

Farfesa Abubakar ya godewa Manajan Daraktan kuma ya yi alkawarin ba da hadin kai ga hukumar.

]]>
https://freedomradionig.com/za-mu-tabbatar-ruwan-fanfo-ya-isa-ko-ina-a-kano-md/feed/ 0 51859
Hisbah: Mun bada wa’adin mako 2 ga masu aikata baɗala domin tuba https://freedomradionig.com/hisbah-mun-bada-waadin-mako-2-ga-masu-aikata-ba%c9%97ala-domin-tuba/ https://freedomradionig.com/hisbah-mun-bada-waadin-mako-2-ga-masu-aikata-ba%c9%97ala-domin-tuba/#respond Tue, 05 Mar 2024 15:58:30 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51854 Babban kwamandan Hisbah Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya koma ofishinsa domin ci gaba da aiki bayan ɗinke barakar ta kunno kai tsakaninsa da Gwamnatin kano.

Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya jagoranci raka shugaban hukumar Malan Aminu Daurawa.

Yayin shigar shi ofishin Malam Aminu Ibrahim daurawa ya ce wannan ɓaraka da ta kunno kai tsakanin sa da gwamnatin Kano wasu mutane ne da basa son ci gaban kano suka ƙirƙire ta domin mayar da kano koma baya.

Haka zaliha yace yanzu haka an ɗinke duk wata ɓaraka da aka samu tsakani wanda hakan ya ƙarawa hukumar ƙaimi wajen ci gaba da gudanar da aikin su ka’in da na’in.

Daura ya ce duk wasu mutane da suka san suna aikata baɗala to hukumar ta basu wa’adin mako 2 domin tuba in ba haka ba duk wanda suka kama to dole doka tayi aiki akan sa.

Da yake jawabi Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa yace wannan sasancin da akayi zai kawo karshen baɗala a jihar Kano.

A nasa ɓangaren farfesa Muhammad Babangida da ya kasance guda cikin wa’inda suka shiga zaƙanin sasancin yace wannan sasancin da akayi ba ƙaramin ɗaga darajar Kano zaiyi ba.

Haka zalika an buƙaci al’ummar jihar kano dama ƙasa baki ɗaya da su kasance masu sanya idanu wajen kan tarbiyyar ƴaƴan su domin samun al’umma na gari da ciyar da kano gaba

]]>
https://freedomradionig.com/hisbah-mun-bada-waadin-mako-2-ga-masu-aikata-ba%c9%97ala-domin-tuba/feed/ 0 51854
Za mu samarwa da matasa hanyoyin dogaro da kai-Gwamnatin Kano https://freedomradionig.com/za-mu-samarwa-da-matasa-hanyoyin-dogaro-da-kai-gwamnatin-kano/ https://freedomradionig.com/za-mu-samarwa-da-matasa-hanyoyin-dogaro-da-kai-gwamnatin-kano/#respond Tue, 05 Mar 2024 02:20:07 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51877 Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da mayar da hankali wajen koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai ba wai sai mutum ya jira aikin gwamnati.

Inda yanzu haka tsarin da Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yiwa cibiyar koyar da sana’o’i ta Dangote dake Dawakin Kudu zai ɗaga darajar Kano zuwa gaba.

Shugaban cibiyar Alkasim Husaini Wudil ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na ƙara horar da matasa sana’o’in dogaro da kai.

Alkasim Husaini Wudil ya kuma ce a baya wannan cibiyar a kulle take ba’a iya gudanar da komai a cikin ta illa kawai biyan mutane albashi ba tare da sunayin aiki ba.

Adan haka gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagoranci Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin gyara duk wata matsala domin farfaɗo da cibiyar dan samarwa da matasa hanyoyin da zasu dogara da kan su- a cewar Alkasim Husaini Wudil.

Haka kuma yanzu haka cibiyar ta fara aiki gadan gadan ga al’umma inda yanzu haka gwamnati ta samar mata da motocin da zasu dunga jigilar malamai da ɗalibai kyauta ba tare da biyan kuɗi ba.

Haka kuma cibiyar zata dunga yaye ɗalibai mataki mataki kan fannin kwarewar mutum.

Kuma yanzu haka wannan cibiyar ta tanadi duk wasu kayan aiki da za su koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai.

]]>
https://freedomradionig.com/za-mu-samarwa-da-matasa-hanyoyin-dogaro-da-kai-gwamnatin-kano/feed/ 0 51877
Yanzu-yanzu: An yi sulhu tsakanin Abba Kabir da Shiekh Aminu Daurawa https://freedomradionig.com/yanzu-yanzu-an-yi-sulhu-tsakanin-abba-kabir-da-shiekh-aminu-daurawa/ https://freedomradionig.com/yanzu-yanzu-an-yi-sulhu-tsakanin-abba-kabir-da-shiekh-aminu-daurawa/#respond Mon, 04 Mar 2024 22:05:56 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51839 Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi sulhu tsakanin sa da babban kwamandan hukumar Hisba Shiekh Aminu Ibrahim daurawa.

A daren ranar Litinin ne tawagar Malamai daga ƙungiyoyi daban daban suka raka Shiekh Daurawa zuwa fadar Gwamnati.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an yi doguwar tattaunawa ta tsawon awa guda, kafin a kai ga sulhunta shugabannin biyu.

Tuni dai Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya amince da komawa bakin aikin aikinsa, domin ci gaba da jagorantar hukumar Hisba.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’a ne aka wayi gari da ganin faifan bidiyon Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda a ciki ya sanar da ajiye muƙamin sa na babban kwamandan hukumar Hisba.

Matakin nasa na zuwa ne kwana guda biyo bayan wasu kalamai sa gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ga me da yadda hukumar Hisba ke tafiyar da ayyukan ta.

Kuma sulhun ya samu nasara ne bayan da ɓangaren zauren haɗin kan Malamai da ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano suka bibiyi abinda ya faru tare da yin tsayin daka wajen kamo bakin zaren.

]]>
https://freedomradionig.com/yanzu-yanzu-an-yi-sulhu-tsakanin-abba-kabir-da-shiekh-aminu-daurawa/feed/ 0 51839
Da ɗumi-ɗumi – Sheikh Aminu Daurawa ya ajiye muƙaminsa na Babban Kwamandan Hisbah a Kano https://freedomradionig.com/da-%c9%97umi-%c9%97umi-sheikh-aminu-daurawa-ya-ajiye-mu%c6%99aminsa-na-babban-kwamandan-hisbah-a-kano/ https://freedomradionig.com/da-%c9%97umi-%c9%97umi-sheikh-aminu-daurawa-ya-ajiye-mu%c6%99aminsa-na-babban-kwamandan-hisbah-a-kano/#respond Fri, 01 Mar 2024 08:16:49 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51836 Babban Kwamandan hukumar Hisba a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye muƙaminsa.

Da safiyar ranar Juma’a ne Daurawa ya wallafa wani bidiyonsa da ya yi cikakken bayani kan ajiye muƙamin.

Cikin bidiyon an jiyo Daurawa na neman afuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa abin da yayi na kuskure yayin aikin sa a hukumar Hisba.

“Allah ya sa ni ba ni da wani ƙudiri illa naga matasa sun samu tarbiyya da gyara irin na Musulunci, hakan ne ya sa na rinƙa kiransu muna tattaunawa don samar da gyara, muna da aljihuna na rinƙa ƙoƙarin kyautata musu” a cewar Daurawa.

Ya kuma ce “Ina Kaduna na samu bayanan da Gwamna ya yi a kan aikin mu, kuma hakan ne ya sa na yanke shawarar ajiye muƙamina muka ina godiya da damar da ya bani”.

A ƙarshe Daurawa ya yi fatan alkhairi ga Gwamnan.

]]>
https://freedomradionig.com/da-%c9%97umi-%c9%97umi-sheikh-aminu-daurawa-ya-ajiye-mu%c6%99aminsa-na-babban-kwamandan-hisbah-a-kano/feed/ 0 51836
Zamu ƙarawa limamai kuɗin Alawus ɗin da ake basu https://freedomradionig.com/zamu-%c6%99arawa-limamai-ku%c9%97in-alawus-%c9%97in-da-ake-basu/ https://freedomradionig.com/zamu-%c6%99arawa-limamai-ku%c9%97in-alawus-%c9%97in-da-ake-basu/#respond Thu, 29 Feb 2024 18:59:38 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51831 Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ƙarawa dukkan nin limaman masallatan juma’a kuɗin da ake basu a wata la’akari da yadda abin da ake biyan su yayi kaɗan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da limaman masallatan juma’a dake faɗin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya ce la’akari da irin gudunmawar da limaman suke bayarwa ga addinin musulunci ya sanya gwamnatin jihar Kano zatayi wannan huɓɓasa wajen ƙara musu alawus ɗin da ake basu.

Haka zalika Gwamnan ya buƙaci malaman Addinin musuluncin da ke faɗin jihar kano da su mayar da hankali wajen faɗakar da al’umma abin da addini ya tanadar domin kawowa jihar kano ci gaba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce yawan faɗakar da al’umma da malamai sukeyi na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tarbiyyar al’umma.

Haka kuma gwamnan ya ce wannan ƙarin kuɗin da gwamnati zatayiwa limaman zaizo ne kai tsaye daga ofishin babban akantan kuɗi na jihar

Wasu daga cikin limaman masallatan juma’a dake nan kano sun wannan abu da gwamna zaiyi musu abin a yaba ne.

Wanda hakan zai ƙara karfafa musu gwiwa da ci gaba da gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Haka kuma gwamnan ya ce yanzu haka ya sanya kwamitin da zai sanya idanu wajen kula da ciyarwar azimin watan Ramadana domin samarwa da al’umma sassaucin matsin da ake ciki.

]]>
https://freedomradionig.com/zamu-%c6%99arawa-limamai-ku%c9%97in-alawus-%c9%97in-da-ake-basu/feed/ 0 51831
Abba Gida-Gida – Kuskure yadda Hizbah take kama maza da mata tana watsawa mota https://freedomradionig.com/abba-gida-gida-kuskure-yadda-hizbah-take-kama-maza-da-mata-tana-watsawa-mota/ https://freedomradionig.com/abba-gida-gida-kuskure-yadda-hizbah-take-kama-maza-da-mata-tana-watsawa-mota/#respond Thu, 29 Feb 2024 18:57:06 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51828 Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce Kuskure ne Hukumomi su rika kamo matasa maza da mata suna jefa su a cikin mota wai a matsayin gyara.

Gwamnan yayi wannan jawabin ne yayin da yake ganawa da malaman Addinin Musulunci a fadar gwamnatin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce wannan baiyi daidai da addini ba yadda wani bidiyo yake yawo a kafafen sadarwa na yadda hukuma Hizba taje wani waje a fadin kano harma da wajen da ɗalibai suke a zaune domin kama su, inda a yayin kamen akayi abin da baiyi daidai da addini ba.

Adan haka dole gwamnati tayi duba akan wannan abu da kuma samar da tsari wanda zai samarwa da al’umma musamman matasa tarbiya.

Gwamnan ya kuma ce wa’azi da addu’a shine mafita ga wanda ake ganin baya aikata dai dai ba ko aibata su ba dan haka malamai faɗakarwa ga al’umma na hannun su.

Gwamnan ya ƙara da cewa a wannan lokaci na karatowar azumin watan Ramadan gwamnatin sa tayiwa al’ummar jihar tanadin raba abinci domin rage matsin rayuwa da ake ciki.

Gwamna ya kuma tabbatar da cewa duk wasu masallatan juma’a da suke faɗin jihar nan an gyara su la’akari da yadda wasu masallatan suke babu kyan gani.

Haka kuma yace zai tabbatar da an ƙarawa dukkan nin limaman masallatan juma’a kuɗaɗen da ake biyan su kuma kuɗin zai dunga zuwa ne kai tsage daga ofishin babban akantan kuɗi na jihar domin tabbatar da daidaito.

]]>
https://freedomradionig.com/abba-gida-gida-kuskure-yadda-hizbah-take-kama-maza-da-mata-tana-watsawa-mota/feed/ 0 51828
REMASAB- Taci gaba da feshin maganin sauro a kano https://freedomradionig.com/remasab-ta-%c6%99addamar-da-feshin-maganin-sauro-a-kano/ https://freedomradionig.com/remasab-ta-%c6%99addamar-da-feshin-maganin-sauro-a-kano/#respond Thu, 29 Feb 2024 12:54:44 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51817 Hukumar kwashe shara ta jihar kano ta ƙaddamar da feshin maganin sauro a ƙaramar hukumar Nasarawa domin samin saukin cututtuka ga al’umma musamman na zazzaɓin cizon sauro

Shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ne ya jagorancin feshin maganin sauron a unguwar Badawa dake ƙaramar hukumar Nasarawa.

Ahmadu Zago, wanda ya dami wakilcin Darakta tsare-tsare na hukumar Alhaji Yahaya Sani Abbas, ya ce sun kaddamar da aikin feshin maganin sauron a yankin Badawa, don dakile cutukan da sauro ke yadawa ga al’umma.

Ya kara da cewa za’a tabbatar an yi feshin maganin a dukkan nin lunguna da sako na unguwar Badawa, kamar yadda gwamanan jahar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kudiri aniyar hidimta wa al’umma ta bangarori da dama don samun nutsuwa da walwala a gidajen su.

Haka kuma za’a ci gaba da shiga dukkannin unguwannin da suke a faɗin jihar Kano domin ganin su anyi musu wannan feshin, don rage yaɗuwar cutuka a faɗin jihar.

]]>
https://freedomradionig.com/remasab-ta-%c6%99addamar-da-feshin-maganin-sauro-a-kano/feed/ 0 51817
Yan Kasa Cikin Halin Ni ƴasu-Yospis https://freedomradionig.com/yan-kasa-cikin-halin-ni-%c6%b4asu-yospis/ https://freedomradionig.com/yan-kasa-cikin-halin-ni-%c6%b4asu-yospis/#respond Tue, 27 Feb 2024 14:56:47 +0000 https://freedomradionig.com/?p=51813 Gamayyar kungiyoyin da suka hadar da na Aminu Magashi da kungiyar matasa dake yaki da cutuka masu yaɗuwa da sauran al’amura ta Yosip, sun nuna takaicinsu kan yadda ‘yan kasa ke cikin mawuyacin hali akan tsadar rayuwar da suke fuskanta.

Shugabar kungiyar ta Yosip Zainab Nasir Ahmad ta ce duk da gudunmawar da suke bayarwa a fannin lafiya, ilimi, tattalin arziki
Al’ummar kasar nan na cikin wani hali la’akari da halin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.

Wanna dai na zuwa ne a Yayin da ake bukin tunawa da irin rawar da kungiyoyin da ba na gwmanati ba ke takawa a fadin duniya a dukkanin ranar 27 ga watan Faburelu, wasu kungiyoyi masu zaman kansu a nan Kano suka nuna takaicin su, kan yadda al’ummar kasar nan ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da yan kasa ke fuskanta.

A nasa bangaren mai bawa gwamna shawara a nan Kano Alhaji Nasiru Isa Dikko, ya ce sun karbi koken kungiyoyin, kuma zai gabatar da shi a inda ya dace domin daukar mataki na gaba.

 

]]>
https://freedomradionig.com/yan-kasa-cikin-halin-ni-%c6%b4asu-yospis/feed/ 0 51813